Yau Talata, kungiyar tsaro ta NATO ta nuna hotuna shaidar cewa hari da ta kai ta sararin samaniya a Libya, ta auna shine kan wata cibiyar sadarwa ta soja, duk da ikirarin da gwamnatin Libya tayi cewa farar hula NATO ta kai wa hari.
Kakakin kungiyar Mike Bracken, ya fada yau a birnin Naples, cewa harin da kungiyar ta kai jiya litinin a Surman, ana amfani da wurin ne wajen kitsa hare hare kan farar hula. Ya nuna hotunan ginin da akan gidan akwai gofofi da sandunan tauraruwar dan’adam, inda ake shirya kai hare hare.
Amma gwamnatin Libya tace harin ya aukawa gidajen kwanane na wani aminin shugaba Moammar Gadhafi. Tana ikirarin harin ya kashe mutane 15.
Ahalin yanzu kuma, China ta bayyana fatan zata taimaka wajen gano bakin zare a rikicin na Libya a lokacin shawarwari da zatayi cikin makon nan da wakilin gwamnatin ‘yan tawaye.
Kakakin ma’aikatar harkokin 3ajen kasar Hong Lei yace shawarwarin da za’a yau Talata d a gobe laraba da manzon ‘yan tawaye Mahmoud Jibril ya nuna burin China na ci gaba da tuntunbar duka sassan biyu a rikicin na Libya.