Kungiyar Kawance ta NATO ta fadi jiya Litini cewa ta kaddamar da hari kan wata babbar cibiyar bayar da umurnin soji a Libiya, a sa’ilinda gwamnati kuma ke fadin cewa harin ya ruguza wani babban ginin zaman iyali mallakin wani babban aminin shugaban Libiya Muammar Gaddafi.
Da farko dai kungiyar kawancen ta karyata batun harin, tana mai cewa ita ba ta kaddamar da wata harkar soji a ‘yan kwanakin nan a wuraren Surman, mai tazarar kilomita 65 yamma da Trabulus, babban birnin kasar.
Gwamnatin ta Libiya ta ce NATO ta kai hari kan katafaren ginin Khoweidi al-Hamid, ta kashe mutane 15, ciki har da akalla biyu daga cikin jikokinsa da matarsa.
An ce shi al-Hamidi, wanda mamba ne na Majalisar Gudanarwar Juyin Juya Halin Libiya da ke bisa jagorancin Mr. Gaddafi – ya tsira ba ko kwarzani. Wannan mutum mai tasiri ya taka rawa a juyin mulkin day a kawo shugaban na Libiya bisa gadon mulki. Diyarsa na auren daya daga cikin ‘ya’yan Gaddafi mai suna Saadi Gaddafi.
NATO dai t ace bat a iya tantance zargin rasa rayukan ba. Zargin na Libiya na baya bayan nan ya zo ne kwana guda bayan da NATO ta amince cewa mai yiwuwa wani harin da ta kai ya hallaka fararen kaya a babban birnin kasar ta Libiya.
A halin da ake ciki kuma, wata kafar yada labaran gwamnatin China t ace Mustafa Abdel-Jalil, shugaban Majalisar Gudanarwar Shugabancin Wucin Gadi ta ‘yan tawayen, ya isa Beijing a yau Talata don ziyarar kwanaki biyu.
A farkon wannan watan dai China ta tattauna da wani wakilin Gaddafi, kuma jami’an diflomasiyyar China sun gana da ‘yan tawayen a birnin Benghazi.