Jam’iyya mai mulkin kasar Senegal ta yi watsi da yunkurin da ta yi na sauya tsarin mulkin kasar a bayan da magoya bayan jam’iyyun suka tayar da kayar baya a Dakar, babban birnin kasar.
Masu zanga-zangar sun yi arangama da ‘yan sandan kwantar da tarzoma yau alhamis a lokacin da suka fito domin tabbatar da cewa ba a sauya tsarin mulkin ba.
‘Yan hamayya suka ce gyara dokokin zabe zai sa shugaba Abdoulaye Wade ya samu saukin ci gaba da zama a kan karagar mulki. Tsarin mulkin yanzu ya tanadi cewa tilas ne kafin a tabbatar da mutum a zaman shugaban kasa sai ya samu akalla kuri’a guda fiye da rabin dukkan kuri’un da aka kada. Jam’iyya mai mulkin kasar ta yi kokarin rage yawan kuri’un da aked bukatar mutum ya samu zuwa kashi 25 cikin 100 kawai na dukkan kuri’u idan har ya fi sauran ‘yan takara yawan kuri’u.
Shirin sauya tsarin mulkin kuma ya nemi kirkiro da sabon mukamin mataimakin shugaban kasa, kujerar da masu hamayya suka ce ana nufin kirkiro ta ne ma dan shugaba Wade.
Ministan shari’a na Senegal, Cheikh Tidiane, ya fadawa ‘yan majalisar dokokin a yau alhamis cewa za a bar dokar zaben kamar yadda take yanzu a cikin tsarin mulki. Tun da fari, an shafe tsawon sa’a guda ana arangama a tsakanin ‘yan sandan kwantar da tarzoma da masu zanga-zanga.