Shugabannin Afirka sun bude taron kolin da ake sa ran zai fi mayar da hankali kan rikicin da ake yi a kasar Libya. Ana wannan taron kolin ne a kasar Equatorial Guinea.
Wani kwamiti na shugabannin kasashen Afirka biyar yana kokarin tsara wani shirin kawo karshen rikicin, wanda kuma za a gabatar a gaban taron kolin domin neman amincewarsa. Shirin ya kunshi kiran da a tsagaita wuta a Libya tare da shirya zabe na dimokuradiyya.
Su kuma ‘yan tawayen Libya su na son shirin ya kunshi kiran da shugaba Muammar Gaddafi na Libya yayi murabus nan take. Wakilan ‘yan tawaye da na gwamnatin shugaba Gaddafi su na halartar wannan taron kolin kwanaki biyu.
Haka kuma, shugabannin na Afirka zasu tattauna halin da ake ciki a kasar Sudan. An shirya Kudancin Sudan zata zamo ‘yantacciyar kasa a ranar 9 ga watan Yuli, amma kuma sassan su na gwabza fada a wasu sassan na bakin iyakarsu.