Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cimma Yarjajjeniya Kan Yankin Abyei Na Sudan

Wakilan Arewaci da Kudancin Sudan kenan ke rattaba hannu kan yarjajjeniyar.
Wakilan Arewaci da Kudancin Sudan kenan ke rattaba hannu kan yarjajjeniyar.

An cimma wata muhimmiyar yarjajjeniya a tattaunawar da ake tsakanin arewaci da kudancin Sudan kan makomar yankin Abyei mai arzikin man fetur da ake takaddama akai kasa da sati uku kafin ranar samin ‘yancin kudu.

Jami’ai sun rattaba hannu akai a jiya Litini a Habasha bayan tattaunawar tsawon kwana da kwanaki da wani sa’in kan zo da sarkakkiya, bisa jagorancin tsohon shugaban Afirka ta kudu Thabo Mbeki. Yarjajjeniyar ta tanaji janye sojoji kwakwata daga yankin na Abyei a maye su da dakarun kiyaye zaman lafiya na Habasha.

Da arewa da kudun sun kuma amince su kafa wani kwamitin bai daya na tabbatar da tsaro Abyei din.

Mr. Mbeki ya gaya wa manema labarai cewa yarjajjeniyar ta share fagen dawowar dubban mutanen da aka tarwatsa. An tsai da shawar tattaunawa ta dindindin kan makomar Abyei bayan kudancin Sudan ya zama mai cin gashin kai a ran 9 ga watan Yuli.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Victoria Nuland t ace Amurka ta yi na’am da yarjajjeniyar sannan ta nemi da dukkannin bangarorin sun aiwatar da yarjajjeniyar da yadda za a sami sahihin yanayin tsaro da ingantacciyar rayuwar jama’a.

Nuland ta kuma yi kira ga dukkannin bangarorin su daina fada ba tare da bata lokaci ba a jihar kudancin Kordofan da ke kan iyaka, inda dakarun gwamnati su ka yi ta gwabzawa da sojojin da ke dasawa da kudu.

XS
SM
MD
LG