Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ebola: NCDC Ta Tsaurara Sanya Idanu Kan Iyakokin Najeriya

A makon daya gabata, ma’aikatar lafiya ta Uganda ta tabbatar da barkewar annobar da ta yi sanadiyar mutuwar mutum guda yanzu kuma take bin sawun mutane 44 da ya yi mu’amala da su.

Hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya (NCDC) ta tsaurara matakan sanya idanu akan hanyoyin shigowa kasar sakamakon sabuwar barkewar cutar Ebola a Uganda.

A makon daya gabata, ma’aikatar lafiya ta Uganda ta tabbatar da barkewar annobar da ta yi sanadiyar mutuwar mutum guda yanzu kuma take bin sawun mutane 44 da ya yi mu’amala da su.

Sakamakon hakan, NCDC a cikin shawarwarin data fitar tace duk da cewar babu cutar a Najeriya, amma tana aiki ne domin dakile shigowarta.

Shugaban NCDC ya bayyana cewar, “ganowa da wuri, da tsame masu fama da ita daga cikin jama’a da kirkirar dabarun tallafawa masu fama da ita su warke da kuma dabarun dakile ta a asibitoci tare da bin diddigi da sanya idanu akan mutanen da suka mu’amala da masu fama da cutar, na matukar rage yaduwarta da kuma yiyuwar mutuwa sakamakonta.”

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG