Dakarun burged ta 6, na rundunar sojin Najeriya dake aikin wanzar da zaman lafiya mai taken “Operation Whirl Stroke” a shiya ta 3, sun yi dirar mikiya a kan wani sansanin ‘yan bindiga da ya yi kaurin suna tare da hallaka wani mutum da ake zargin dan bindiga ne a Angwan Bala, da ke gundumar Kambari ta karamar hukumar Karim Lamido, a jihar Taraba.
Al’amarin wanda ya faru a Lahadin da ta gabata ya biyo bayan samun bayanan sirrin da rundunar sojin Najeriya ta yi.
Ta hanyar amfani da sahihan bayanan sirri game da motsin mutanen da ake zargin ‘yan bindiga ne, dakarun sun gudanar da sintiri domin gano maboyar, kuma hango tawagar sojojin yasa ‘yan bindigar bude wuta, abin da ya sabbaba mayar da kwakkwaran martani nan take daga sojojin.
A yayin musayar wutar, an hallaka dan bindiga daya, yayin da wasu 23 da suka hada da maza 19 da mata 4 suka mika wuya ba tare da wata turjiya ba.
Hakan na kunshe ne a sanarwar da mai rikon mukamin mataimakin daraktan yada labarai na burged ta 6, Kyaftin Oluodunde Oni ya fitar.
Kyaftin Oni ya kara da cewa cikakken binciken da aka gudanar a sansanin ya kai ga kwato dimbin mukamai da albarusai, ciki har da bindigogi kirar AK-47 guda 4 da kwanson harsashai guda 5 da jigida 20 ta harsashin musamman da karamar bindiga kirar Ingilishi da bindigogi 2 kirar gida da adduna 28 da babura 16 da wukake 48.
Dandalin Mu Tattauna