Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NLC Ta Jingine Zanga-Zanga Kan Karin Kudin Kiran Waya

Shugaban NLC, Joe Ajaero (Hoto: Facebook/NLC)
Shugaban NLC, Joe Ajaero (Hoto: Facebook/NLC)

Bayan tattaunawa mai tsawo, bangarorin 2 sun amince da kafa wani kwamiti mai wakilai 10 da zai kunshi mutum 5 daga bangaren gwamnatin Najeriya sai mutum 5 daga bangaren NLC su sake nazarin binciken tare da mika rahoto cikin makonni 2.

Kungiyar Kwadago a Najeriya (NLC) ta jingine zanga-zangar da take shirin yi akan karin harajin kiran waya da sayen data da kasso 50 cikin 100.

An yanke wannan shawara ne bayan da kungiyar kwadagon ta gana da tawagar gwamnatin tarayya karkashin jagorancin sakataren gwamnatin Najeriya, George Akume, a jiya Litinin.

A cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai da hulda da jama’a a ofishin sakataren gwamnatin, Segun Imohiosen, manufar ganawar ita ce samar da natsuwa a bangaren kwadago tare da kare muradan ‘yan najeriya.

Ya kara da cewar ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Muhammad Idris, wanda ya zanta a madadin gwamnatin tarayya, yace manufar ganawar ita ce nazartar binciken da hukumar ncc mai kula da kamfanonin sadarwa a Najeriya tayi wanda ya kai ga karin kaso 50 cikin 100 kan harajin kiran waya da sayen data.

Bayan tattaunawa mai tsawo, bangarorin 2 sun amince da kafa wani kwamiti mai wakilai 10 da zai kunshi mutum 5 daga bangaren gwamnatin Najeriya sai mutum 5 daga bangaren NLC su sake nazarin binciken tare da mika rahoto cikin makonni 2.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG