Mr, Andrew Walye tsohon sakataren gwamnatin jihar Adamawa, shine ya furta hakan ga taron manema labarai a Yola, cewa wanda ake tuhumar a bara ya gabatar da takardar koke ga hukumomin tsaro kan wasu bindigogo da aka kwato daga hanun ‘yan Boko Haram, amma aka karkatasu ba tare an mika su ga hukuma ba wanda har yanzu ba a gudanar da bincike ba.
Bincike da wakilin Muryar Amurka, ya gudanar ya nuna cewa baya ga zargin karkata makamai da ‘ya’yan kungiyar ke yiwa juna, akwai wani batun na rub-da-ciki kan kudin tallafi da gwamnati ke baiwa kungiyar wanda ya sa ta dare biyu - inji Mal. Ephraim Abdullahi.
Da yake amsa tambayar ko gaskiya ne rabon tallafin da gwamnati ke baiwa kungiyar na daga cikin dalilin da suk yi wa juna tonon silili Alhaji Yakubu Ali, ya tabbatar da haka kamar yadda da zaku ji a cikin sauti cikin rahotan da ke kasa.