Tashin bom din ya faru ne a jiya lokacin da ake sallar Asuba, inda wasu da ake zargin cewa ‘ya ‘yan kungiyar Boko Haram ne mata suka kutsa cikin wani masallaci suka tayar da boma boman dake jikinsu, yayinda daya daga ckin matan ta tayar da nata cikin masallaci, ita kuma dayar ta tayar da nata ne a gindin bishiya inda take ta kukan neman taimako daga isowar mutanen ne ta tayar bom din dake jikinta ta hallaka mutane da dama.
Tun da farko dai ansami rahotannin cewa mutane 24 ne suka mutu, yayin da daga bisani aka sami karuwar wasu mutane 3 wanda nan ne akace adadin ya kai 27.
Gwamnan jihar Borno, Hon. Kashim Shettima, ya ziyarci inda aka sami tashin bom din don jajantawa al’umma da wannan abin ya shafa da kuma jan hankulan jama’a da a tashi tsaye wajen kula, domin a baya an tashi tsaye wajen kula musammam a masallatai lokacin sallah inda akan sami wasu mutane na gadin masu sallah, hakan zai kara tabbatar da tsaro kafin ganin an kawo karshen wannan masifa.
Domin karin bayani.