Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Mutum Sama Da Miliyan 7 Suke Bukatar Taimako A Arewa Maso Gabas


Taron Hadin Kan Jami'an Tsaro Da Hukumomin Agaji A Maiduguri
Taron Hadin Kan Jami'an Tsaro Da Hukumomin Agaji A Maiduguri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bude wani taron kwanaki uku a garin Maiduguri na Jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar da ma’aikatar lura da ayyukan jinkai da raya al’uma suka shirya na kyautata dangantaka tsakanin hukumomin tsaro da kuma hukumomin da suke bada agaji a wannan shiya.

Wakilin shugaba Buhari a gurin taron, Ministan Tsaron Najeriya, Mejo Janar Bashir Magashi mai ritaya, ya ce taron an shirya shine don kara kyautata daganata tsakanin sojoji da kuma jami’an da suke bada agajin gaggawa a arewa maso gabashin kasar, saboda irin tsamin dangantaka da ake samu a tsakaninsu.

Itama Ministan ma’aikatar lura da ayyukan jinkai da raya al’uma, Hajiya Sadiya Umar Farouq, tace dole a kyautata danganta tsakanin al’uma da jami’an tsaro da kuma yin aiki tare domin a taimakawa jama’ar da suka samu kansu cikin wannan yana yi.

Shima shugaban hukumar Majalisar Dinkin Duniya na Najeriya, Mr. Edward Kallon, ya ce sama da mutum miliyan bakwai suke bukatar taimako agajin gaggawa a arewa maso gabashin Najeriya, wanda wannan shine adadin mafi girma a duniya na mutanan da suke bukatar taimako.

A lokacin da yake jawabi Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce daga yanzu dole ne mu san wadanda suke shigowa cikin jihar mu domin yin ayyukan jinkai daga ciki da wajan Najeriya.

Saurari cikakken rahoton wakilinmu Haruna Dauda Biu daga Maiduguri:

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG