Darajar naira ta jima tana faduwa tun bayan da farashin man fetur ya fadi a kasuwar duniya.
Man fetur shi ne babban abu da ke samarwa Najeriya kudaden shigarta hakan kuma ya yi tasiri matuka akan tattalin arzikin kasar.
Shirin na CBN ya maida hankali wajen ba wasu zababbun bankuna damar lura da harkar canji ta yadda farashin dala zai kasance bisa yadda kasuwa ta yi halinta.
Wannan mataki dai ya sha yabo a wurin wasu, yayin da kuma wasu su ke sukar shi matakin.
Suma masu hadahadar canjin kudi masu zaman kansu ba a barsu a baya ba wajen tofa albarkacin bakinsu dangane da wannan lamari.
A wannan hirar da za ku ji, Grace Alheri Abdu ta tambayi Alhaji Abbas Muhammad mai canjin kudi a Abuja, irin tasirin da wannan mataki zai iya yi a rayuwar talakawa: