Yawancin garuruwan dake makwaftaka da birnin Abuja da suka fito daga jihohin Neja da Nasarawa da Kaduna da kuma Kogi suna fama da matsaloli daban daban na karancin ababen more rayuwa.
Dan majalisar dattawan Najeriya David Umaru dake wakiltar gabashin jihar Neja, a wani taron manema labarai a Minna yayi karin haske kan dalilinsu na neman gwamnatin tarayya ta kafa hukuma ta musamman da zata kula da irin wadannan garuruwan.\
Yace suna son a kirkiro wata hukuma ce da zata dinga kula da matsalolin garuruwan. Yawancin ma'aikatan dake aiki a Abuja suna zaune cikin irin wadannan garuruwan ne. Basu da isasshen ruwan sha da hanyoyi, abubuwan da kan iya rage wahalar da jama'a ke sha saboda yawan jama'a. Bai kamata a dorawa jihohin dake kewaye da Abuja wannan wahalar ba.
Shi ma shugaban kwamitin labarai na majalisar dokokin jihar Neja Onarebul Sha'aibu Liman dan yankin Suleja mai makwaftaka da Abuja yace samarda hukumar ko ma'aikatar nada anfani bisa la'akari da dimbin jama'a dake zaune a yankin. Yace babu inda za'a zagaya a masarautar Suleja da ba za'a ga dimbin jama'a ba da suka zo cin albarkacin birnin tarayya.
Ga karin bayani.