Sabon sakataren ya bukaci da a gudanar da wani taron gaggawa na kasashen mambobin kungiyar domin tattaunawa kan yadda farashin man ke kara faduwa.
A cikin kwanakin nan ne ma kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta duniya, wato, OPEC, ta sanar da Mohammed Barkindo daga Najeriya a matsayin sabon Sakatare Janar na kungiyar.
Barkindo, wanda ya maye gurbin Abdalla El-Badri dan kasar Libya , wanda ke rike da mukamin tun shekarar 2007,yace dole kasashe su tashi tsaye
Shugaban kungiyar ya fada a wani ganawa da yayi da manema labarai a filin saukan jiragen sama na kasa da kasa dake Yola. Yace akwai bukatar karatun ta natsu game da yadda darajar mai dama iskar gas,ke kara faduwa a kasuwannin duniya.
Shugaban kungiyar ta OPEC, yace ‘’ Wannan al'amari dai ya zo ne a daidai lokacin da farashin man fetur ke ci gaba da faduwa a kasuwannin duniya. Kuma dole a tashi tsaye don fuskantar kalubalen dake akwai.
‘’Da farko ma dai dole mu daura damara ta hanyar samun hadin kai da fahimtar juna a tsakanin membobin kungiyar ta OPEC,don tinkaran wadannan matsaloli ba wai kawai ga OPEC ba,kai harma da fannin man fetur da kuma iskar gas.
‘’Kuma na san kasata Najeriya zata yi duk abun da ya kamata ta ga an samu wakilci na gari,’’ a cewarsa.
To sai dai kuma daa juya ga hare haren yankin Neja –Delta, sabon Sakatare Janar din,ya nuna kaduwarsa game da abubuwan dake faruwa,da yace hakan na jawo wa Najeriya babbar asara.
Ga karin bayani
.