Saudiyya ta kammala shirye-shiryen karbar alhazan aikin hajjin bana, yayin da aka dauki tsauraran matakai na kariya daga coronavirus.
Daga cikin kusan mutane dubu dari biyar da suka nemi izini, dubu sittin ne kadai aka amince su yi aikin na bana, a cewar Abed al-Haibi na kamfanin kula da alhazai, Rawahel.
Ya ce babban abin da aka fi mayar da hankali akai a aikin na bana shi ne kare lafiyar alhazai.
Karin bayani akan: hajjin bana, coronavirus, COVID-19, NAHCON, da Saudiyya.
"Babu shakka hajjin bana ya sha banban da wanda aka saba gani. Babu wani mai aikin hajji dai zai iya zuwa wurare tsarkaka, illa ta hanyoyin hudu da hukumomi suka amince da su, wadanda suka hada da Al zaidy,, al Naseem, al shara’i, da al nouriya.
Sannan mahajjata ba za su iya shiga kowanne sansani ba, illa ta hanyoyi masu na’urorin zamani da aka tanada, wadanda aka samarwa katin da za a yi amfani da su wajen ratsa su.
Akwai akalla mutum rabin miliyan daya da suka nemi iznin zuwa aikin hajjin bana, amma ma’aikatar ta amince da dubu 60 kadai.
Abin da ma’aikatarmu ta saka a gaba shi ne, a kare lafiyar mahajjata, shi ya sa muka gindaya wasu sharudda da suka hada da yanayin lafiyar mutum, shekarunsa, sannan mutum ya tabbatar ba shi da wata babbar cuta.
Kazalika, wannan shekara, ta sha banban da shekarun baya dangane da abinda ya shafi abinci, wanda za a rika shirya shi tun gabanin a bukaci yin amfani da shi."
Labarai masu alaka
Zangon shirye-shirye
-
Disamba 20, 2024
Ana Ci Gaba Da Fama Da Karancin Takardan Naira A Najeriya
-
Disamba 20, 2024
Hira Da Audu Bulama Bukarti A Birnin Landan Na Kasar Birtaniya
-
Disamba 07, 2024
Yadda Aka Kirga A WaninRumfar Zabe A Greater Accra
-
Disamba 07, 2024
An Fara Kirga Kuri'un Zaben Ghana