Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Mu Fara Tattaunawa Kan Hajjin Badi Da Hukumar Aikin Hajji Da Umrah Ta Saudiya - NAHCON


NAHCON
NAHCON

Hukumar alhazan Najeriya NAHCON ta bayyana cewa za ta fara tattaunawa da hukumar aikin hajji da umrah ta Saudiyya don fara yarjejeniyar aikin hajjin badi.

BORNO, NIGERIA - NAHCON ta bayyana haka ne a taron bitar aikin Hajjin da ya gabata da ya samu halartar masu ruwa da tsaki na lamuran aikin Hajji a Najeriya.

“Ina farin cikin sanar da ku cewa ba kamar aikin Hajjin da ya gabata ba da a ka fara shiri a makare don rashin samun bayanai daga Saudiyya, ma’aikatar aikin Hajji da Umrah ta shaida mana cewa shirin aikin Hajjin badi zai fara ne ta taron na’urar yanar gizo, ta faifan bidiyo da za a gudanar a ranar 21 ga watan Disamba tsakanin mu da saudiyya” Inji shugaban hukumar alhazan Zikrullah Kunle Hassan.

NAHCON
NAHCON

Ya kara da cewa an shirya taron ne da zummar tattaunawa don gano irin kalubalen da aka fuskanta a aikin Hajjin 2022 don a kuma samo hanyoyin da za a hana faruwan hakan nan gaba.

Shugaban kwamitin Alhazai a majalisar dokokin Najeriya Wakili Abubakar Hassan Nalaraba ya bayyana wasu daga cikin kalubalen da aka fuskanta a aikin hajjin 2022.

Shugaban kungiyar JIBWIS ta Najeriya Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce irin wannan taron yana da muhimmanci tare da yin kira ga hukumar NAHCON data kara bawa malamai fifiko don karantar da alhazai yadda zasu gudanar da aikin Hajji karbabbe.

Sheikh Abdullahi Bala Lau, Leader of JIBWIS
Sheikh Abdullahi Bala Lau, Leader of JIBWIS

A nasa bangaren, shahararren mai wa’azin Islama Malam Kabiru Gombe ya yaba da yadda alhazai ke bada hadin kai wajen yin tambayoyi ga malamai kan wani abu da ya shige musu duhu game da aikin Hajji.

NAHCON ta kuma bada lambar yabo ga jihohin da suka yi fice a gudanar da aikin Hajji. Za’a fara aiwatar da asusun adashen gata da mutane kan biya kudi kadan-kadan har su tara kudin da zasu iya samun biyan kujeran hajji.

Kwanan nan ‘yan NAHCON suka je Indonesiya don gani da ido kan harkar asusun bisa daukar nauyin bankin raya musulunci mai helkwata a Jidda.

XS
SM
MD
LG