Tun a tsakiyar watan jiya ne gwamnatin Nijar ta fara ayyukan mayar da ‘yan gudun hijirar jihar Diffa zuwa garuruwansu na asali bayan da a daya gefe hukumomin suka tsaurara matakan da suka bada damar shayo kan matsalar tsaro a yankunan da rayuwa ta yi wuya a can bayan sanadiyar ayyukan kungiyar Boko Haram.
Ziyarar wace ke matsayin ta farko da Mohamed Bazoum ke kaiwa daya daga cikin jihohin wannan kasa tun bayan hawansa karagar mulki a watan Afrilun 2021 wani abin alfahari ne a wajen al’umar jihar Diffa injisu.
Jihar Diffa mai makwaftaka da jihohin Yobe da Borno na samun bakuncin ‘yan gudun hijirar Najeriya kusan 300,000 wadanda suka tserewa rikicin Boko Haram shekaru fiye da 7.
Saboda haka shugaba Mohamed Bazoum da gwamnan jihar Borno Farfesa Baba Gana Umara Zulum suka yi mahada a birnin Diffa don tattauna hanyoyin soma kwashe ‘yan Najeriya zuwa gida.
Wannan ziyara ta na matsayin matakin baiwa ‘yan gudun hijirar cikin gida goyon baya da za ta kasance wata dama ga shugaban kasar Nijar domin tattaunawa da shugabanin al’umomin yankin Diffa akan batun farfado da harakokin yau da kullum irinsu noma da kiwo da kamun kifi musamman a garuruwan dake kewayen Tafkin Chadi inda matsalar tsaro ta fi kamari a shekarun baya.
Sannan zai kai ziyara a garin Baroua inda a tsakiyar watan Yuni hukumomi suka mayar da ‘yan garin sama da 5,000 bayan kwashe shekaru da dama suna hijira a kewayen garin Diffa.
Saurari rahoto daga Souley Moumouni Barma: