Shugaban kungiyar gwamnonin shiyyar Arewa maso Gabas, kuma gwamnan jihar Borno Farfesa Bàbagana Umara Zulum ne ya bayyana hakan a jawabin bude taron kungiyar gwamnonin shiyyar karo na hudu da aka gudanar a Bauchi.
Taron wanda hudu daga cikin gwamnonin shiyyar guda shida sun halarta in banda gwamnonin jihohin Taraba da na Yobe, sun gabatar da sanarwan bayan taro guda takwas da suka hada har da batun tsaro, da na rashin samar da ayyukan ci gaba a yankin,da batun aikin wutar lantarki na Mambilla.
Mataimakin shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Adamawa, Amadu Fintiri shi yakaranta jawabin bayan taron.
Ya bayyana cewa, wannan kiran bai nuna sojojin Najeriya sun gaza ba, sai dai neman taimakon sojoji daga makwabta zai kara mafu karfin yakar kungiyar da ta buwayi yankin.
Kungiyar gwamnonin ta ce yin haka zai taimaka wajen murkushe 'yan kungiyar cikin kankanen lokaci ya kuma bada dama ga manoma su koma gona, matasa kuma su sami ayyukan yi, jihohin kuma su ci gaba.
Mai masaukin baki ,gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Muhammed, yayi bayani game da batun jami’an tsaro na al’umma da kuma batun samar da wutan lantarki na Mambilla. Bisa ga cewar shi, jami'an tsaron al'umma za su taimaka wajen shawo kan matsalar tsaro da ake fuskanta a jihohin kasar.
Kungiyar Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati Wal-Jihad, da aka fi sani da Boko Haram da ake kyautata zaton ta fara hadan kan masu tsats-tsaurin ra'ayin addinin Islama ne a garin Maiduguri cikin shekara ta 1999 karkashin jagorancin Mohammed Yusuf , ta kai kazamin hari na farko ne a shekara ta 2003 lokacin da mayaka sama da 200 su ka kai hare hare kan ofisoshin 'yan sanda a jihar Yobe.
A shekara ta 2009 kungiyar ta fara daga hankali a garin Bauchi da nan da nan ya bazu zuwa jihohin Borno, Kano da kuma Yobe. Tun daga wannan lokacin ake fama da hare haren kungiyar musamman a jihohin Borno da Yobe, da kuma wadansu kasashe da ke makwabtaka da Najeriya.
Saurari rahoton Abdulwahab Mohammed cikin sauti:
Karin bayani akan: jihar Borno, Boko Haram, Nigeria, da Najeriya.