Musulmi za su kwashe baki dayan watan suna azumi, inda za su gujewa ci da sha da jima’i a cikin yini, yayin da za su dukufa wajen gudanar da ibadu da ciki har da karatun Al Qur’ani mai tsarki.
A wasu lokuta al’adu da banbancin yanki, kan sa a samu sabanin yadda ake gudanar da azumin na ramadana a wasu sassan duniya.
Gudanar da azumin ya kan zama da wuya ga wasu yankunan duniya, musamman inda rana ta kan dauki lokaci kafin ta fadi, ko kuma ma bata faduwa musamman a lokutan bazara, wanda hakan ya sa wasu malamai suka yi ittifakin cewa irin yankunan da ranar ba ta faduwa kan iya yin amfani da lokacin Saudiya wajen shan ruwa da yin sahur.
Kamar a sauran sassan duniya, anan Amurka ma Musulmi sun dukufa wajen sa idon wajen neman watan na Ramadana.
Kakakin cibiyar Musulunci da ke Charlotte a jihar North Carolina, Jibril Hough, ya ce, duk da cewa musulmi ba su da rinjaye a Amurka, watan na ramadana kan ba da wata dama da Musulman su ke taruwa a masallatai maimakon a gidajensu domin shan ruwa, kamar yadda ake gani a wasu sassan duniya.