Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Musulman Amurka Sunce Zasu Fito Su Kada Kuri'a A Zaben Shugaban Kasa


Musulman Amurka
Musulman Amurka

Wani bincike da aka gudanar anan Amurka ya nuna cewa kashi 86% na Musulmin dake kasar duk sun kudurta cewa zasu fito su jefa kujrik’unsu a zaben shugaban kasar da za’ayi ran 8 ga wata mai fita na Nuwamba, a daidai lokacinda ake ganin kamar kyamar da ake nunawa Musulmi da Musulunci na karuwa a Amurka din.

Kungiyar kare Hakkokin Musulmi ta Amurka da ake kira CAIR ce a jiya ta fito da alkalumman dake nuna sakamakon wannan binciken, inda kuma aka nuna cewa daga cikin kashi 86% din, akshi 72% duk sun yanke shawarar ‘yar takarar shugaban kasa ta jam’iyyar Democrats, Hillary Clinton ce suke shirin baiwa kuri’unsu, yayinda kashi 4% suka ce zasu jefa wa jam’iyyar Republican, Donald Trump nasu kuri’un.

Akwai kuma 3% da suka ce su kam ‘yar takaran jam’iyyar Green Party, Jill Stein ce zasu zaba, sannan kashi 2% na karshe kuma suka ce hankalinsu ya fi kwantawa da Gary Johnson, dan takaran jam’iyyar Libertarian Party.

XS
SM
MD
LG