Shi kuwa abokin hamayyar Musuveni Kizza Besigye ya samu kashi 35 ne yayin da daya tankarar mai suna Amama Mbabazi ya samu kashi 1.4.
Akalla kashi 63 na masu kada kuri’a ne suka je rumfunan zabe a cewar hukumar zaben kasar wacce ta bayyana sakamakon na karshe.
An fidda wannan sakamakon zabe ne sa’o’i kadan, kafin karewar wa’adin bayyana shi ya cika.
Wani mai sa ido daga kungiyar tarayyar kasashen Turai, ya ce mamaye gurbin siyasa da jam’iyya mai mulki ta yi ya tasiri akan zaben, kana ya yi zargin cewa hukumomi sun yi barazana ga masu zabe da ‘yan takara a ranakun zabe da kuma kwanakin da suka biyo baya.
Rahotanni na nuni da cewa an yiwa Besigye daurin talala saboda zaman dardar da ake yi a kasar.