Yayin da a Najeriya ake ci gaba da fuskantar matsalolin da suka shafi harkar tsaro, wadanda suka hada da yaki da Bokom Haram da na ‘yan bindiga da kuma masu garkuwa da mutane, hukumomin taro na ikrarin suna samun nasara a yaki da ta'addanci.
A wata hira ta musamman da yayi da Muryar Amurka, Shugaban rundunar sojojin saman Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar, ya ce duk wanda zai yi la’akkari daga "inda aka faro da kuma inda ake a yanzu lallai zai san gwamnatin Najeriya tana kokari sosai."
"Idan aka tuna a shekara hudu ko biyar da suka gabata "bama bomai suna tashi kusan ko ina a cikin kasar nan kamar a Nyanya da ke babban birnin tarayya Abuja har sau biyu bam yana tashi da hedkwatar ‘yan sandan kasar da dai sauran wurare a cikin birnin," a cewar Air Marshal Sadique Abubakar.
Ya kuma kara da cewa cikin ikon Allah saboda irin kokarin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta yi saboda irin damuwa da al’amari, ya ba da umurnin a dauki duk matakan da suka kamata saboda a ga an kare rayukan mutane da dukiyoyinsu.
Saurari cikakkiyar hirar da Aliyu Mustapha Sokoto ya yi da Shugaban rundunar sojojin saman Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar:
Facebook Forum