A Najeriya batun ingantattun hanyoyi na cikin abinda ya dauki hanakalin Majalisar Dattawa, ganin cewa samun kudaden gina su yana nema ya gagari kundila.
Wannan shi ne dalilin da Komitin Kula da ayyuka a karkashin Sanata Adamu Aliero ya ce, ya shirya tsaf wajen ganin an dawo da shirin karbar harajin iyakar shiga gari a manyan hanyoyin da ke cikin fadin kasar, wanda aka fi sani da “Tollgate” a turanci.
A zamanin mulkin tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo ne aka kashe makudan kudade har Naira Miliyan 360, wajen rusa “Tollgate” din da ake da su a iyakar mayan hanyoyi na kasar ba tare da sake gina wasu ba. Shugaban kwamitin kula da ayyuka a Majalisar Dattawa Sanata Mohammed Adamu Aliero ya ce, matakin rusa “Tollgate” din ya ba su haushi, shi ya sa su ka yi binciken domin gano yanda wasu kasashe irin su Malaysia da Marocco da Ghana su ka gina hanyoyin su, kuma sun gano cewa a Najeriya ne kadai za ka bi hanya mai tsawon kilomita 200 babu karbar harajin da ke shiga aljihun Gwamnati a matsayin hanyar kudaden shiga da za a yi amfani da su wajen gina kyawawan hanyoyi.
Wanan shi ne dalilin da ya sa za su hada hannu da ‘yan kasuwa wajen gina sababbin “Tollgate”.
A wani bangare kuma Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya Sanata Uba Sani ya ce, dole ne kwamitocin Majalisar Dattawa su hada hannu wajen samo wa Gwamnatin tarrayya Kudaden shiga da za su taimaka wajen farfado da tattalin arzikin kasar, idan har za a cika alkawalin da shugaba Mohammadu Buhari ya yi, na ceto ‘yan kasa miliyan 100 daga cikin matsanancin talauci.
Ga masu nazari a fanin tattalin arzikin kasa irinsu Alhaji Abubakar Ali, ya ce, duniya ta cigaba, domin nan da dan lokaci kadan za a daina amfani da saye da sayar da man fetur a matsayin hanyar samun kudaden shiga, domin yanzu haka akwai ma'adinai masu yawa da za a sayar da su da makudan kudade inda za a samu haraji akansu, har su taimaka wajen gina tattalin arzikin kasar.
Abin jira a gani shi ne, tasirin da dawo da harajin shiga gari ta manyan hanyoyin kasar, duba da irin matakan da za a gindaya wajen hana yin sama da fadi ko almundahana da kudaden harajin idan an tara su.
Ga cikakken rahoton Wakiliyar Muryar Amurka daga Abuja, Madina Dauda
Facebook Forum