Kakakin Rundunar, Air Commodore Ibikunme Daramola ya fada a cikin wata sanarwa da ya aikewa muryar Amurka cewa wasu daga cikin 'yan bindigar sun arce zuwa kan tsaunin Janko inda nan ma jirgin yakin ya bisu ya gama da su.
Wannan farmakin dai na zuwa ne bayan wani hari da 'yan bindiga suka kaiwa wasu dakarun Najeriya a kauyen Sunke dake karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara, da kuma kaurar da 'yan bindigar ke yi zuwa yankin Birnin Gwari
Mr. Daramola ya ce hedkwatar rundunar da ke yaki da 'yan bindiga a shiyyar Arewa Maso Yammacin Najeriya wato Operation Hadarin Daji, ta bada umarnin sabunta kaiwa 'yan ta'addan farmaki ne don ci gaba da kare dukiya da rayukan al'umma.
Massanin tsaro Farfesa Mohammed Tukur Baba, Dan Iyan mutum biyu ya ce irin wannan dabarar ce sojojin Amurka suka yi amfani da ita a yakin Vietnam, inda ake ragargaza abokan gaba ta sama.
Farfesa Tukur ya ce ya na da kyakkyawar fata wannan karon za a gama da 'yan ta'addan da irin wannan farmaki ta sama.
Ga karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum