A ranar Lahadi sojoji a kasar Guinea suka kifar da gwamnatin kasar.
Ga muhimman lokuta a tarihin kasar wacce ke yammacin nahiyar Afirka tun bayan da ta samu ‘yancin kai daga Faransa a shekarar 1958.
1958: Samun ‘Yancin Kai
A ranar 2 ga watan Oktoba, 1958, Ahmed Sekou Toure ya ayyana samun ‘yancin kan Guinea, kwanaki kadan bayan zaben raba gardama da aka yi, wanda sakamakonsa ya yi watsi da kasancewar kasar a kungiyar renon Faransa wacce tsohon shugaban kasar Charles de Gaulle ya samar.
A watan Janairun 1961, aka zabi Sekou Toure a matsayin shugaban kasa. A shekarar 1967 kasar ta Guinea ta koma turbar bin tsarin mulkin ‘yan gurguzu.
Toure Ya Kwashe Shekara 26 A Kan Mulki
Toure, wanda ake masa kallon “uba a fagen samun ‘yancin kai” ya koma daga gwarzo a idon duniya zuwa mutum mai mulkin kama-karya, inda aka zarge shi da batan kusan mutum dubu 50,000, a cewar kungiyoyin kare hakkin bil adama. Kazalika daruruwan mutane sun tsere daga kasar.
1984-2008: Zamanin Mulkin Conte
A ranar 3 ga watan Afrilun 1984, mako guda bayan mutuwar Toure, sojojin kasar suka karbe mulki karkashin jagorancin Kanar Lansana Conte.
A shekarar 1985 ya dakile wani yunkurin juyin mulki da kuma wani mummunan bore da wasu sojoji suka yi a 1996.
A shekarar 1993 aka zabi Conte a matsayin shugaban kasa aka kuma sake zaben shi sau biyu a wani zabe mai cike da rudani wanda bangren ‘yan adawa suka kauracewa.
A farkon shekarar 2007, aka yi wata zanga-zangar adawa da “tsarin mulkin Conte” wacce gwamnatinsa ta dakile, sanadiyyar hakan, har mutum sama da 180 suka mutu, a cewar kungiyoyin kare hakkin bil adama.
Juyin Mulkin 2008
A ranar 23 ga watan Disambar 2008, sojoji suka karbe mulki cikin lumana kwana guda bayan mutuwar Conte sanadiyyar wata cuta da ba a bayyana ba. Ya mutu yana da shekara 74.
A lokacin, gwamnati ta yi mubaya’a ga shugaban sojojin da suka yi juyin mulki Moussa Dadis Camara.
A watan Satumbar 2009, jami’an tsaro suka bude wuta kan dubban ‘yan adawa da suka taru a wani filin wasa don gudanar da gangami.
A watan Disamba, aka raunata shugaban sojojin da suka karbi mulki Camara, bayan da wani daga cikin manyan hadimansa ya harbe shi a ka.
An Rantsar Da Alpha Conde A Matsayin Shugaban Kasa A 2010
A watan Janairun 2010, shugaban rikon kwarya Sekouba Konate ya rattaba hannu a wata yarjejeniya da Camara, inda aka shirya zaben shugaban kasa.
A ranar 7 ga watan Nuwamba, Alpha Conde ya zama shugaban Guinea na farko da aka zaba bisa tsarin dimokradiyya.
Conde ya taba kubuta daga wani hari da aka kai gidansa da ke Conakry babban birnin kasar a ranar 19 ga watan Yulin 2011.
An sake zaben sa a ranar 11 ga watan Oktobar 2015, zaben da ya kasance mai cike da tarzoma da zargin magudi.
Barkewar Cutar Ebola A Shekarar 2013
A shekarar 2013 cutar Ebola ta barke wacce ta kai har shekarar 2016 kafin a shawo kanta inda ta hallaka sama da mutum 2,500.
Wa’adin Mulki Na Uku
Daga Oktoban 2019, yunkurin yin wa’adin mulki na uku da Conde ya sa a gaba ya haifar da zazzafar adawa, inda aka kashe dumbin masu zanga-zanga.
Kasar Guinea ta amince da wani sabon kundin tsarin mulki a ranar 22 ga watan Maris din 2020, bayan wani zaben jin ra’ayin jama’a da aka gudanar wanda ‘yan adawa suka kauracewa wanda kuma ya ba Conde damar yin takarar neman wa’adi na uku.
A ranar 18 ga watan Oktoba aka ayyana Conde a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar, yayin da Cellou Dalein da sauran ‘yan hamayya da suka kara da Conde suka yi korafin an tafka magudi.