Jami'in ya kara da cewa Goita ya isa sansanin sojoji na Kati, a wajen Bamako, "inda aka karfafa tsaro".
Wasu mutane biyu dauke da makamai, ciki har da wanda ke rike da wuka, suka afkawa Goita a cikin babban masallacin da ke Bamako babban birnin kasar, kamar yadda wani dan jaridar AFP ya gani.
Harin ya faru ne a lokacin da ake addu’o’in bukukuwan Musulunci na Eid al-Adha.
Ministan Harkokin Addini Mamadou Kone ya shaida wa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP cewa wani mutum ya "yi kokarin kashe shugaban da wuka" amma sai aka cafke shi.
Latus Toure, darektan Babban Masallacin, ya ce wani maharin ya yi wa shugaban kawanya amma ya ji wa wani rauni maimakonsa.
Nan da nan AFP ba ta iya tabbatar da abkuwan hakan ba.
Kasar ta Mali dai tana ta kokarin shawo kan wata kungiyar jihadi da ta fara bullo kai a arewacin kasar a shekarar 2012, kuma tun daga lokacin ta bazu zuwa kasashen Burkina Faso, Mali da Niger.
An kasha dubun-dubatar sojoji da fararen hula sannan daruruwa sun tsere daga gidajensu.
Kanar Goita ya jagoranci juyin mulki a cikin watan Agustan da ya gabata, inda ya hambarar zababben shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita bayan makonni da aka kwashe ana zanga-zangar adawa kan cin hanci da rashawa da kuma rikicin jihadi da aka dade ana yi.
A watan Mayu, ya hambarar da gwamnatin rikon kwarya da aka damka wa jagorantarmulkin kasar don sake komawa hannun farar hula a watan Fabrairun 2022.
Daga nan aka sanya shi shugaban rikon kwarya, amma ya yi alkawarin ci gaba da cika burinsa na komawa ga farar hula.