Da ta ke jawabi ta kafar bidiyo a babban taron manema labarai daga hedikwatarta da ke Brazzaville, Janhuriyar Congo, Daraktar hukumar ta WHO shiyyar Afurka, Matshidiso Moeti, ta ce jami’ai na kuma sa ran samun karin zubi 8,600 na alluran rigakafi daga Amurka, wanda zai sa jimlar alluran rigakafin ya kai 20,000.
Haka kuma hukumar na sa ran isar alluran zuwa ranar Lahadi, sannan kuma za a fara rigakafin Ebolar zuwa ranar Litini.
Jami’an lafiya a kasar ta Guinea, sun ayyana tsananin cutar yanzu a matsayin annoba a ranar Lahadi, bayan da aka kara samun karin mutane biyu da su ka kamu da cutar a Gouecke, wani kauye a lardin N’Zerekore.
A kalla mutum guda ya mutu a wurin. Wannan ne barkewar Ebola a karon farko tun bayan na 2016, lokacin da aka yi nasarar kawar da wata babbar annobar Ebolar.