Matsayar kenan da kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta cimma a taron da ta yi, inda gwamnonin kungiyar suka tabbatar cewa tsarin kiwo da Fulani makiyaya ke yi ba zai iya ci gaba ba a wannan zamani.
Biyo bayan tashe-tashen hankulan dake faruwa da ya hada da Fulani makiyaya a wasu sassan Najeriya, kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta kuduri aniyar magance faruwar hakan ta hanyar samar wa Fulani makiyaya wuraren da za su zauna su kuma yi kiwon dabbobinsu.
Da yake yi wa sashen Hausa na Muryar Amurka karin bayani, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce gwamnonin sun yi wa matasansu alkwarin samar da mafita ga matsalar tashin hankali da ta shafi Fulani makiyaya. Wanda hakan ne ya sa suka gano cewa barin Fulani na ci gaba da yawace-yawacen kiwo bai kamata ba, ganin cewa yanzu zamani ya sa yawan mutane da ma dabbobi na ci gaba da karuwa.
Gwamna Masari ya ce jihohin Arewa sun shirya samar wa Fulanin matsuguni a kowace jiha, tare da samar musu wuraren da zasu ke kiwon dabbobinsu tare da sayar da madara da nono da mai, amma sai sun fara tuntubar gwamnatin tarayya domin samun hadin kanta.
Domin cikakken bayani saurari hirar wakilin Muryar Amurka, Umar Faruk Musa da Gwamna Aminu Bello Masari.