A ziyarar da babban Hafsan Sojojin Najeriiya, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, ya kai garin Ngamdu a jihar Borno, ya ce za su hada kai da sojojin kasar Chadi don kawo karshen mayakan Boko Haram da ke addabar shiyar Arewa maso gabashin kasar.
Manjo Attahiru, ya dai bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a garin na Ngamdu. Ya dai gana da jami'an sojin da ke karkashin kulawarsa da ma yi musu alkawarin za a inganta aikinsu, da kuma samar masu kayan aiki don magance wannan matsala ta 'yan ta'adda; sai kuma ya tabbatar da cewar za a share musu hawayensu akan duk wasu matsaloli da ke damunsu.
Ya dai kara da cewar shugaban kasa na nuna damuwarsa da yadda ayyukan ta'addanci ke cigaba da habaka a yankin, wannan shi ne babban dalilin da yasa ya ke wannan ziyarar da kara karfin gwiwa ga sojojin.
Haka kuma sabbin tsare-tsare da suka fito da su ba wai don wani abu ba ne, illa su kawo karshen wannan yakin, don hakan idan aka duba aikin rundunar sojin ta Tura Ta Kai Bango, za a ga cewar an samu nasarori da dama. Su na so su ga an dora daga inda aka tsaya akan yaki da ta'addanci.
Daga Maiduguri ga rahoton Haruna Dauda Biu, a cikin sauti.
Karin bayani akan: Manjo Janar Ibrahim Attahiru, jihar Borno, Nigeria, da Najeriya.