Yunkurin ganin an cire kungiyar ISIS, daga birnin Raqa, inda take ikirarin babbar hedikwatar ta a Syria zai zamo a sahun farko na abinda Tillerson zai tattauna a ziyarar tasa a Ankara, kamar yadda jami'an Amurka ke cewa.
A cikin shugabannin siyasar kasar wadanda Tillerson, zai gana dasu sun hada da shugaba Recep Tayip Erdowan.
Goyon bayan da Washington, ke baiwa 'yan awaren Kurdawan Syria, na PYD da kuma sojojin su, nasa kai da ake kira YPG, a yaki da akeyi da kungiyar ISIS, zaici gaba da kasancewa batun dake da dinbin tasiri a Ankara, wanda hakan kuma ke ci gaba da sukar alaka da PKK, mai fada da gwamnati ta Turkiyya.
Wannan yasa wani sheihin malami daga cibiyar Carnergia, dake Turai, yace akwai batutuwa da dama baibaye da batun na Syria. wannan yasa kasar Turkiyya, tasa rai cewa abubuwa zasu canza lokacin da aka bayyana zaben Shugaba Donald Trump, a matsayin shugaban Amurka.
Wannan ne ma yasa jim kadan da Trump, ya karbi ragamar mulki, kasar ta Turkiyya, tayi kokarin ganin ko zata shawo kan sabuwar gwamnatin Amurkan domin ta katse hulda da kurdawa 'yan tawayen Syria, wato PYK Wadda turkiyyar, ke wa kallon kungiyar ‘yan ta'adda amma lamarin bai canza ba.
Facebook Forum