Yayinda Birtaniya ke shirin kwashe tarkacenta daga Tarayyar Turai Muryar Amurka ta nemi jin ta bakin 'yan Najeriya akan makomar kasar da kuma tasirin da wannan ficewar zata yi akan Najeriya.
Alhaji Kasumu Garba Kurfi masanin tattalin arziki dake birnin Legas yace na farko duk wasu yarjeniyoyi da Najeriya tayi da Ingila yanzu dole a koma a sakesu domin lokacin da aka cimmasu an hada da Tarayyar Turai ne. Sai an sake yin wasu da Ingila kawai lamarin kuma da ka iya daukan lokaci. Taimakon da kasar ke samu zasu canza. Yace rabuwar ba abun da ake so ba ne.
Amma Alhaji Abdullahi Abuja Wakilin Zazzan Suleja mai sharhi kan harkokin siyasa da tattalin arziki yana mai cewa kasashen renon Ingila akwai hanyoyi daban daban da zasu ci gajiyar wannan ficewa ta Ingila daga Tarayyar Turai. Yace bayan ta kammala ficewa dole ta dawo kan kasashen da ta rena ta ga yadda zata yi huldan kasuwanci dasu.
Alhaji Abdullahi yace yanzu ma suna da matsala da Tarayyar Turai. Anfanin gona da suka aika sun dawo masu da su wai domin suna da nasu ka'idodin. Sun dawo masu da irin su gyada da wake da dai sauransu. Idan Ingila ta fita daga cikinsu babu ruwansu da dokokinsu sai su kai anfanin gonakinsu Ingila kai tsaye.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.
Facebook Forum