Kasar China ta fada yau Laraba cewa zata cigaba da kiyaye alkawurran da ta dauka a karkashin yarjejeniyar sauyin yanayi ta duniya da aka cimma a Paris, kwana daya bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu a dokar da zata kawas da duk dokokin kiyaye muhalli da tsohon shugaba Barack Obama ya girka.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China Lu Kang, ya ce yin watsi da batun sauyin yanayi babban kalubale ne ga duniya, kuma China zata cigaba da nata kokarin koda sauran gwamnatocin wasu kaashe sun sauya manufofin su.
Sabuwar dokar da shugaba Trump ya sa wa hannu ta maido da zazzafar muhawarar da ake akan yadda hidimomin yau da kullum na Bil Adama ke shafar chanjin yanayi da kuma damuwa akan yadda shekaru da dama da aka kwashe ana kokarin kulla yarjejeniyar shawo kan yanayi a duniya ke neman zama bata lokaci.
Facebook Forum