Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Donald Trump Ya Rattaba Hannu Dan Kawar Da Dokar Amfani Da Makamashi Mara Dumama Yanayi


Shugaba Donald Trump, ya rattaba hannu kan wani umurni bisa ikonsa na Shugaban kasa, wanda ya kawo karshen tsarin nan na amfani da makamashi mara dumama yanayi, wanda na daya daga cikin muhimman manufofin tsohuwar gwamnatin Obama, da aka bullo da su don yaki da dumamar yanayi.

Wannan uwa-uba, ya shafe manufofin Amurka, da shekaru gommai, wadanda ba ma kawai sun tsaya ga batun dumamar yanayi ba ne, amma har ma da na kare muhalli, da kuma ka'idar samar da makamashi da iza makamashin.

Dama a yayin yakin neman zabe, Trump, ya sha cewa zai kawo karshen wannan manufa. Akwai lokacin da ma ya bayyana batun dumamar yanayin da "almara," to amma dai abin da Shugaban ya fi cewa shi ne ka'idojin kare muhalli masu tsauri, na illa ga bangaren samar da makamashi ta yadda ke hana su samun riba, kuma hakan na shafar batun kirkiro ayyukan yi.

Wannan ikon na Shugaban kasa, ya zayyana matakin da Fadar Shugaban Amurka, ta White House, za ta dauka, wajen kawar da duk wani sharadi wanda ke kawo cikas ga samar da makamashi.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG