Hukumar kula da filayen jiragen saman Najeriya (FAAN) ta sanar da rufe titin jirgin sama mai lamba 18R/36L a tashar jiragen sama ta Murtala Muhammad dake legas a mataki na wucin gadi domin gudanar da gyare-gyare.
Rufewar tashar jiragen saman, da aka tsara gudanarwa tsakanin ranakun 3 da 4 ga watan Maris din da muke ciki, na zuwa ne makonni 2 bayan da aka sake budeta sakamakon rufewar watanni 11 da aka yi domin gudanar da gyare-gyare.
A cikin wata sanarwa mai dauke da kwanan wata 28 ga watan Fabrairun 2025, shugaban sashen ayyuka na FAAN, J.U Nwosu ya kafa hujja da damuwa a kan kiyaye afkuwar hadura, inda yace kayan gini akan titin jirgin na iya yin barazana ga jirage masu sauka da tashi.
Sanarwar, da aka aikewa manajan tashar jiragen saman da kuma takwaransa mai kula da shiyar kudu maso yammacin Najeriya, ta jaddada bukatar rufe tashar domin kiyaye afkuwar hadura.
Dandalin Mu Tattauna