Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Natasha Ta Zargi Akpabio Da Cin Zarafinta Ta Hanyar Lalata


Sanata Natasha da Sanata Akpabio
Sanata Natasha da Sanata Akpabio

Tuni Akpabio ya musanta wannan zargi ta bakin mashawarcinsa akan harkokin yada labarai, Kenny Okulogbo.

Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta zargi shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, da cin zarafi ta hanyar lalata.

Tuni Akpabio ya musanta wannan zargi ta bakin mashawarcinsa akan harkokin yada labarai, Kenny Okulogbo.

Sanata Natasha ta yi wannan zargi a hirar da ta yi da tashar talabijin ta Arise a yau Juma’a.

Ta yi zargin cewar Akpabio na hana duk kudirin da ta gabatar a zauren majalisar wucewa saboda taki amincewa da tayin yin lalata da ita.

‘Yar majalisar mai wakiltar jihar kogi ta kara da cewar sakamakon kin amincewa da tayin yin lalatar Akpabio a mahaifarsa ta Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom, da kuma a ofishinsa a Abuja, yake ci gaba da cin zarafinta tare da hantararta babu kakkautawa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG