Kungiyar ta dattawan Borno tace akwai bukatan shugaban kasar Najeriya Muhammad Buhari ya sa baki a takaddamar domin kaucewa irin abun da ka iya faruwa.
Kungiyar tace ta ga abun da ya faru a jihar Borno da kungiyar 'yan ta'adan Boko Haram. Kungiyar tana ganin abun dake faruwa a Kaduna makamancin yadda Boko Haram ta fara ne a Borno.
Ganin cewa jihar Kaduna na tsakiyar Najeriya ne kungiyar ta kira shugaban kasar ya ankara da abun da ka iya faruwa kafin tafiya tayi nisa domin kada a bari wani abu ya sake faruwa a kasar.
Bayan kungiyar ta fitar da sanarwar Dr. Bulama Manu Gubio na kungiyar dattawan ya yiwa Muryar Amurka karin haske.
Yace lokain da 'yan Boko Haram suka fara a Borno gwamnati ta dauki tsauraran matakai maimakon a lallashesu tare da laluma. Ba'a bi hanyar sulhu ba, ba'a kuma shawo kansu ta hanyar doka ba. A lokacin an sa doka an dakatar da addininsu. Bayan hakan kowa ya san abun da ya jawowa jihar da wasu ma dake makwaftaka da ita. Yace addini ba mutum ba ne abun dake zuciyar mutum ne.
Yace dokar Najeriya ta ba kowa 'yancin yin addinin da ya ga dama. Yace su basa goyon bayan 'yan shi'a kuma basu san yadda suke yin addininsu ba. Amma sun ce su musulmai ne. Saboda haka duk wanda yake tada rigima da sunan addini doka tayi aiki a kansa.
Dattawan Bornon sun tsunduma cikin abun dake faruwa a Kaduna ne domin a cewarsu ya shafesu saboda baki daya Boko Haram ta wargaza kasar Borno. Harkokin ilimi da kiwon lafiya da dai sauransu sun koma baya fiye da shekaru hamsin ko dari ma. Yace saboda haka ba sa son abun da ya samesu ya sake samun wani bangaren Najeriya musamman a tsakiyar Najeriya.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.