Hukumar kula da zirga zirgar jiragen sama da ta duniya ICAO ta samo asali ne a daga wani babban taron kasashen duniya da aka gudanar a birnin Chicago na kasar Amurka a shekara ta 1944. Inda a taron aka rattaba hannun dokokin sufurin jirgin sama da keta sata sararin samaniyar kasashe.
Cikin dokokin akwai na rijistar jirage da tabbatar da tsaron fasinjoji da ma sauran ka’idojin da kasashen suka rattabawa hannu don jagorantar bangaren keta hazo.
Idan aka dauke wasu kasashe kalilan da basa karkashin yarjejeniyar yawancin kasashe membobin MDD na mutunta wannan ka’ida. Wanda ya zuwa yanzu anyi bitar ka’idojin har sau takwas domin dacewa da sabon zamani.
A cewar ministan zirga zirgar jiragen Najeriya Hadi Sirika, kasarsa na mutunta dokokin na duniya, ya kuma ce domin tabbatar da tashi da saukar manyan jirage ba tare da tangarda ba dole ne Najeriya ta fadada filayen jirage.
Ministan yace yanzu haka Najeirya na da daukar fasinjoji Miliyan 15 a duk shekara, idan kuma aka kara fadin filayen saukar jiragen kasar tabbas za a iya samun karuwar fasinjoji zuwa Miliyan 60 ko sama da haka.
Domin karin bayani.