Cikin kwanakin nan takaddama tayi tsamari tsakanin rundunar 'yansandan Najeriya da jam'iyyar PDP saboda yanje dogarin gwamnan Rivers da rundunar tayi.
Jam'iyyar ta zargi rundunar da son karya lagon gwamnan jihar a lokacin da za'a yi zaben 'yan majalisar jihar.
Saidai cikin sanarwar da ta aikowa Muryar Amurka tace ta janye DSP Promise Nwosu ne saboda wasu laifuka da kuma rashin da'a. Tace an sami shi dogarin cikin zanga zangar 'yan siyasa a jihar abun da bai dace da aikinsa ba ya kuma karya rantsuwar da yayi a matsayin dansandan Najeriya.
Mataimakin kwamishanan 'yansandan jihar ta Rivers wanda yake sa ido a zanga zangar shi ya hango dogarin cikin masu zanga zangar. Da ya kirashi ya jawo hankalinsa kan rashin dacewar abun da ya keyi sai ya farma mataimakin kwamishanan da fada.
Tuni dai wasu masu sharhi suka ce a matsayinsa na dansanda bai kamata a barshi ya cigaba da kasancewa dogarin gwamnan ba domin shiga zanga zanga ba aikinsa ba ne.
To saidai Dr. Saidu Ahmed Dukawa malami a jami'ar Bayero dake Kano a fannin kimiyar siyasa yace idan gwamnan na wajen zanga zangar tare da dogarin to bai kamata a tuhumi dogarin da laifi ba saboda yana aikin kare gwamnan ne saidai idan babu gwamna a wurin.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.