‘Yan adawar dai na zargin shugaba Isuhu Mahamadu da taka dokar da tayi tanadin kason musamman ga jinsin mata a duk lokacin da ake nade naden mukamin shugabancin al’umma.
Da take bayyana matsayinta game da karar da ‘yan Majalisar Dokokin kasa na bangaren adawa suka shigar game da halaccin gwamnatin mai kunshe da mata 8 daga cikin mambobi 43. Kotun tsarin mulkin kasar ta bayyana cewa dokar da tayi tanadin kason musamman ga mata a kundin tsarin mulki, bata fayyace zahirin adadin kason da ya kamata a basu ba, hakan yasa kotun tace bata da hurumin yanke wani hukunci kan korafin.
Kungiyoyin mata sunce sunyi na’am da abin da kotun tsarin mulkin ta fada. shugabar kungiya Maryama Musa, tayi kira da a shirya wani zaman sulhu da bangaren zartarwa domin kawo karshen wannan lamari.
Kamar yadda abin yake a kowacce kasa ta demokaradiyya, tsarin shari’a a Nijar yayi tanadin wasu hanyoyin da wasu ‘yan kasar dake fatan a warware musu dukkan wasu abubuwan da suka shige musu duhu kan sha’anin doka.
Tun a washegarin nade naden mambobin gwamnatin na ranar 19 ga watan Oktobar shekara ta 2016, kungoyin mata ke ta nuna rashin gamsuwa ga adadin matan da aka baiwa mukami a sabuwar gwamnatin saboda a cewarsu an tauye musu hakki, ganin yadda abin da aka basu ya gaza da kashi 25 daga cikin 100 da doka ta tsara. Lamarin da ya kaisu ga yin zaman dirshan a ofishin ministar ci gaban mata.
Domin karin bayani.