Haka kuma, a cikin hukuncin da ta zartas a jiya, wannan kotun ta ce su ma wasu mutane biyar da ake kara tareda tsohon shugaba Morsi, a sake musu shara’a sabuwa.
A shekarar 2012 Mohammed Morsi yayi abin tarihin zama shugaban kasar Masar na farko da aka zaba ta hanyar demokradiya, amma ko shekara daya baiyi akan karagar mulkin nashi ba, aka sauke shi bayanda aka yi ta shirya tarukkan zanga-zanga, ana zarginsa da cewa yana neman yayi babakere a harakar mulkin Masar, ga shi kuma ya kasa tada komadar tattalin arzikin kasar.
Babban kwamandan sojan kasar Misran a lokacin, Abdel Fatteh el-Sissi ne ya jagoranci wannan gangamin yi wa Morsi bore, kafin shi kansa ya zo ya dare kan karagar mulkin.
Sai dai duk da wannan hukuncin na jiya Talata, Morsi zai ci gaba da zama a gidan wakafi.