A sabon matakin data dauka, farashin galan na mai dana diesel ya karu daga kobo 67 zuwa dala daya da kobo 68. Farashen galan na kananzir kuma ya karu daga kobo 56 zuwa kusan kobo casi’in.
Abdulai Bayraytay, mai magana da yawun shugaban kasar Saliyo Ernest Bai Koroma, ya ce cire tallafin ya zama dole don magance matsalar koma bayan kudaden shiga da kasar take fuskanta sanadiyyar annobar cutar Ebola wadda ta shafi sashen yawon bude ido, da faduwar kuma farashen karfen ore.
Bayraytay ya ce a lokacin da gwamnatin kasar karkashin jam'iyyar APC ta karbi mulki a shekarar 2007, babban gurinta shine farfado da tattalin arzikin kasar don jan hankalin masu saka hannun jari daga kasashen ketare wanda hakan zai sa a sami ayyukan yi a kasar.
Ya kuma ce, don a iya samun damar shawo kan koma bayan tattalin arzikin, gwamnatin kasar ta yi aiki da kawayenta kamar su bankin duniya da asusun bada lamuni don rage kudaden da gwamnati take kashewa a kasar.