Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Siyasan Ghana Sun Kai Ma Juna Hari


Mutanen da suka taru kofar gidan dan siyasa, wato dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta NPP da aka kaiwa hari
Mutanen da suka taru kofar gidan dan siyasa, wato dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta NPP da aka kaiwa hari

Kungiyoyi da daidaikun mutane na cigaba da yin tur da harin ada aka kai kan gidan dan takarar jam'iyyar adawa ta NPP Nana Akufor Ado

Kungiyoyi da gwamnatocin Amurka da na Birtaniya duk sun yi tur da arangaman da ya auku tsakanin magoya bayan NDC jam'iyyar dake mulki da NPP jam'iyyar adawa wanda yayi sanadiyar kai hari gidan dan takarar adawan.

Rahotanni da suka fito daga Ghana sun nuna an yi amfani da kai harin kan gidan dan takarar da wasu muggan makamai.

Ofisoshin jakadancin Amurka da na Birtaniya sun kira a kai zuciya nesa a kuma yi kokarin samun zabe mai adalci cikin kwanciyar hankali. Suna kira a tabbatar da zaman lafiya.

Yamutsi a gaban gidan dan takarar jam'iyyar NPP a Ghana
Yamutsi a gaban gidan dan takarar jam'iyyar NPP a Ghana

Dangane da wannan arangamar Amurka ta bayyana bakin cikinta da abun da ya faru. Mai magana da yawun ofishin jakadancin Amurka tace suna allawadai da duk wani tashin hankali da ya faru sanadiyar zaben dake zuwa. Tace yakamata 'yan kasar ta Ghana su kaucewa duk wani tashin hankali a daidai lokacin da kasar ke shirin gudanar da zabe ranar bakwai ga watan gobe.

Amurka ta kira 'yan takaran da magoya bayansu da su gujewa duk abun da ka kawo tashin hankali lokacin zabe da kuma bayansa. Ta kirasu su warware duk wani rikici dake tsakaninsu ta hanyar shari'a.

To saidai jakadan zaman lafiya na zaben kasar Ribadu Ibrahim da aka tambayeshi akan lamarin sai yace ba'a tabbatar da gaskiyar maganar ba amma ya kara da cewa mutane su rungumi zaman lafiya su guji tashin hankali.

Ga rahoton Baba Makeri da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG