Shugabannin ‘yan tawayen Libiya sun bukaci hukumomin Aljeriya su taso masu keyar matar shugaban Libiya Muammar Gaddafi da uku daga cikin ‘yayansa, bayan da su ka shiga kasar ta Aljeriya da safiyar jiya Litini.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Aljeriya ta bayar da sanarwar cewa matar Gaddafi Safiya, da diyarsa A’isha, da kuma biyu daga cikin ‘yayansa, Mohammad da Hannibal, sun ketara cikin kasar da mota. Su ka ce haka zalika surukai da kuma jikokin shugaban na Libiya su ma sun isa kasar.
Hukumomi a Aljeriya sun ce sun sanar da Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya da kuma Majalisar shugabancin wuccin gadin Libiya. A baya shugabannin ‘yan tawaye sun zargi kasar ta Aljeriya – wadda it ace kadai makwabciyar Libiya a Arewacin Afirka-- da cewa tan a goyon bayan Mr. Gaddafi tare da samar mashi sojojin haya don murkushe tawayen. Aljeriya dai ta karyata zargin.
Har yanzu dai ba a ga shugaban na Libiya bat un bayan da ‘yan tawayen su ka kwace babban birnin kasar a makon jiya, to amman Fadar shugaban Amurka ta White House t ace bat a da wata masaniya mai nuna cewa Gaddafi ya bar Libiya. Haka zalika, ba a san inda sauran ‘ya’yan Gaddafi das u ka taka rawa a harkokin soji da tattalin arzikin kasar ba.
A halin da ake ciki kuma wata kungiyar rajin kare hakkin dan adam da ke Amurka t ace ta gano wata shaidar aikata laifukan yaki da dakarun Gaddafi su ka aikata a Misrata.