Majalisar gudanawarwar gwamnatin wucin gadi ta ‘yan tawayen Libya, ta bada sanarwar ta kauradda aikace aikacenta daga Bengazi zuwa Tripoli, babban birnin kasar.
Jami’in majalisar, Ali Tarhouni, mai kula da harkokin kudi ya fada jiya Alhamis cewa, “wan nan ne takun farko a fara aikin zartaswar majaliar a Tripoli”.
Wan nan sanarwa tazo ne a dai dai lokacinda shugaban kasar Moammar Gadhafi wadda ke tsaka mai wuya, yake kara kira ga magoya bayansa su tashi tsaye wajen murkushe wadanda suke neman hambareshi daga mulki. A cikin wani gajeren jawabi da yayi jiya Alhamis, shugaba Gadhafi ya kira abokan adawarsa da cewa su “beraye ne, ya kuma yi Allah wadai da kasashen waje da suka tsoma kansu cikin wan nan rikici.
Ahalin yanzu kuma, ana ci gaba da gwabza fada tsakanin magoya bayan Gadhafi da ‘yan tawaye a birnin Tripoli. A unguwarda ake kira Abu salim , da akace nan ne tungar magoya bayan Gadhafi a birnin, ‘yan tawaye suna kai somamen neman magoya bayan shugaban. An bada labarin karin mayakan ‘yan tawaye suna isowa Tripoli domin kawo doki ga wadnada suke can, a dai dai lokacinda aka ce ‘yan tawayen sun tasamma Sirte mahaifar kanal Gadhafi, inda magoaya bayansa suka taru da nufin ganin abind a zai turewa buzu nadi. Ahalin yanzu kuma ministan tsaron Britaniya Liam Fox, ya fada jiya Alhamis cewa NATO tana tallafawa ‘yan tawaye wajen farautar Gadhafi. A Washington kuma, MHWA tace ta hakikance cewa makamai masu guba da kuma sinadaran Uraium da Libya ta mallaka basu fada hanun miyagu ba.
A gefe daya kuma Amurka da Afirka ta kudu sun cimma ‘yarjejeniya da zata bada damar a saki dala milyan dubu daya da rabi daga dukiyar Libya da aka sakawa takunkumi ga ‘yan tawayen kasar domin ayyukan jinkai.