Katun manyan Laifuffukan kasa da kasa za ta cigaba da shari’ar wasu jigajigan ‘yan Kenya 6 da ake alakantawa da mummunan tashin hankalin day a biyo bayan zabe a kasar.
Kotun ta yanke hukunci a yau Talata cewa zarge-zargen na da tushe, ta yi watsi da bukatar gwamnatin Kenya cewa ta kori karar.
Alkali Daniel David Ntanda Nsereko y ace kafin a dau kara a matsayin mai iya koruwa, dole ne ya zamana akwai wani shirin bincike na kasa baki daya kan mutanen da ake zargin.
Wannan hukuncin ya tabbatar da hukuncin da aka zartas watanni uku das u ka gabata cewa gwamnati bat a gabatar da shaidar cewa tan a bincike ko kuma gurfanar da mutane shidan da ake zargi.
Mutane 6 da ake zargin sun hada da manyan ‘yan siyasa da hamshakan ‘yan kasuwa da ake zargi da hanu a tashe-tashen hankulan das u ka biyo bayan zaben Kenya na karshen shekarar 2007 da kuma farkon shekarar 2008.