Wata tawagar da ta kunshi motoci akalla 200 dauke da dakarun da ke biyayya ga tsohon shugaban Libiya Muammar Gaddafi ta ketara zuwa cikin kasar Niger da su ke makwabtaka, a daidai lokacin da dakarun da ke adawa da Gaddafin ke ta kara taruwa a wajen gari daya tilo da ya rage a hannun hambararren Shugaban.
Rahotanni daga Niger a yau dinnan Talata sun ce motocin sojin sun nufi babban birnin kasar, Niamey, bayan da su ka kutsa cikin Niger da yammacin Litini. Babban birnin kasar na wata kusurwar kudu maso yammacin kasar ne daura da Burkina Faso, a inda jami’an gwamnatin kasar su ka yi tayin mafaka ga Mr. Gaddafi cikin makwanni biyu da su ka gabata.
Shugaban rukunonin dogarawan tsaron Mr. Gaddafi mai suna Mansour Dhao da wasu ‘yan Libiya din ne da dama su ka fara ketarawa cikin Niger din kafin tawagar ta ketara.