A safiyar jiya litinin, ma’aikatar harkokin wajen Aljeriya ta bada labarin cewa uwargidan shugaban Libya Safiya Moammar Gadhafi, da ‘ya’yansa uku, Aisha da Mohammed da Hannibal, sun tsallaka kan iyaka da mota suka suka shiga Aljeriya.
Shugabannin ‘yan tawayen Libya suka ce zasu bukaci hukumomin Aljeriya da su tusa musu keyarsu zuwa Libya.
Jami’an Aljeriya suka ce sun shaidawa babban sakataren majalisar dinkin Duniya da majalisar gudanawar ‘yan tawaye wannan bayanan. A baya jami’an ‘yan tawaye sun zargi Aljeriya makwabciyar Libya daga arewaci ita kadai ce bata amince da majalisar ‘yan tawayen ba, kuma tana goyon bayan Gadhafi har da samar mishi sojojin haya da nufin murkushe bore da ake masa. Aljeriya ta musanta wan nan zargi.
Har yanzu babu labarin inda shugaban na Libya yake, da wasu daga cikin ‘ya’yansa maza. Manyan ‘yan tawaye jiya litinin suka bada labarin cewa sai ta yiwu an kashe dan shugaban kadhafin Khamis,kwamandan rundunar soji ta musamman, a wani artabu da aka yi ranar Asabar a kudancin birnin Tripoli. An sha bada labarin mutuwarsa sau tarin yawa tun barkewar rikicin kasar, amma an kasa tabbatar da haka.