Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Asabar Din Nan Musulmin Duniya Zasu Fara Azumin Watan Ramadan


Akasarin al'ummar Musulmi a fadin duniya su na shirye-shiryen fara azumin watan Ramadan, wata mai tsarki a Musulunci, daga asabar. Addinin Musulunci yana amfani da bayyanar wata wajen tsaida ranar farko ko ta karshen wata.

Shugabannin addinin Musulunci a fadin duniya sun ce ba a samu ganin wata ba a ranar alhamis, a saboda haka aka tsaida jumma'a ta zamo ranar karshe ta watan Sha'aban.

Musulmi a kasashe kamar Nijeriya, Aljeriya, masar, Indonesiya, Iraqi, Sudan, Syria, Somaliya, kasashen yankin Gulf da yankunan Falasdinawa da ma nan Amurka duk zasu tashi da azumi asabar idan Allah Ya kai mu.

A tsawon watan Ramadan, Musulmi su na gujewa cin abinci ko shan ruwa ko jima'i da wasu abubuwan da dama daga ketowar alfijir har zuwa faduwar rana.

XS
SM
MD
LG