AGADEZ, NIGER - Tawagar ta ziyarci mahimman wuraren da aka kebe domin gina jami’ar Musulunci da kuma wata babbar asibiti mai kula da masu fama da cutar koda da tashar samarda wutar lantarki mai aiki da hasken rana da kuma wasu ayyuka na raya kasa.
Yayin wannan ziyarar, tawagar ta kuma ziyaraci wasu ayyukan da kasar Aljeriya ta soma domin anfanin arewacin Nijar.
Kasar Aljeriya dai tun asali tana da kima a idanuwan al’ummar Nijar sakamakon manyan tsare-tsaren kasar da ta gudanar a kasar ta Nijar.
Masana sun bayyana fatan ganin kasashen biyu sun karfafa dangantaka ta fuskar siyasa da tattalin arziki ta yadda ‘yan kasar Nijar zasu rika gani a kasa aduk wata hulda da gwamnatin mulkin sojan Nijar zata yi tsakanin kasa da kasa musamman kasar Aljeriya da ke zaman babbar kawa ga kasar Nijar wacce suka raba iyaka mai yawa a arewacin kasar.
Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud
Dandalin Mu Tattauna