Ministan harkokin wajen Kuwaiti, ya shaidawa mataimakin shugaban Amurka Dick Cheney, cewa Kuwaiti ba zata goyi bayan duk wani matakin sojan da Amurka zata so dauka a kan Iraqi ba.
Sheikh Sabah al-Ahmed al-Sabah ya ce Kuwaiti ta yanke wannan shawara ba wai domin Iraqi kawarta ce ba, sai dai kawai domin yanayin yanzu bai dace da daukar irin wannan matakin ba. Sheikh Sabah ya ce duk wani matakin sojan da Amurka zata dauka zai yi lahani ga al'ummar Iraqi ne, ba wai kan gwamnatin kasar ba. Jami'in na Iraqi ya ce ya gwammace a kara matsin lamba kan shugaban Iraqi Saddam husseini, ya yarda sufetocin makamai na Majalisar Dinkin Duniya su koma kasar.
Mr. Cheney ya fuskanci adawa da daukar matakin soja kan Iraqi a dukkan kasashen Larabawa 9 da ya ziyarta ya zuwa yanzu, a ranagadin da yake yi na yankin Gabas ta Tsakiya.
Mataimakin shugaban na Amurka yana kokarin lallashin kasashen Larabawa da su goyi bayan matakan sojan da Amurka take tunanin dauka a kan Iraqi, inda hukumomi a Washington ke cewa sun yi imani shugaba Saddam Hussein yana kera makamai masu guba, da na yada cututtuka da kuma na nukiliya. Amurka tayi barazanar daukar mataki idan har Iraqi ba ta kyale sufetocin makamai sun koma kasar ba.
Ita ma Iraqi ta kaddamar da nata yunkurin a fagen diflomasiyya domin karfafa adawar kasashen larabawa ga duk wani matakin sojan da Amurka zata dauka.
Shugaba Saddam Hussein ya tura mataimakin shugaba Taha Yassin Ramadan zuwa Yemen da Sudan. Mukaddashin Firayim Minista Tariq Azeez yana rangadin kasashen Libya, da Tunisiya, da Aljeriya da kuma Morocco. Shi kuma shugaban Babbar majalisar Juyin Juya Hali ta Iraqi, Izzat Ibrahim, ya ziyarci kasashen Jordan, da Sham(Syria), da Lebanon da kuma Misra a makon jiya kafin ya zarce zuwa kasashen yankin Gulf da dama.